Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Tana KOkarin Ganin An Tura Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Zuwa Liberiya - 2003-06-30


Shugabannin Afirka ta Yamma da na MDD sun gana a Abuja, babban birnin Nijeriya, inda suka tattauna kafa rundunar kiyaye zaman lafiyar da za a tura zuwa kasar Liberiya mai fama da yaki.

A jiya lahadi kasashen Afirka ta Yamma suka yi alkawarin bayar da gudumawar sojoji ga wannan runduna, a bayan da babban sakataren MDD, Kofi Annan, ya roke su da su yi hakan.

Amma kuma shugabannin na Afirka ta Yamma suka ce tsoma hannun Amurka shine mataki mafi a'ala a duk wani yunkurin da za a yi na kawo karshen zub da jini a Liberiya.

Shugaba Charles Taylor na Liberiya ya nuna cewa zai yi marhabin ad sojojin kiyaye zaman lafiya na Amurka, amma har yanzu hukumomi a nan Washington ba su nuna wata alamar cewa sojojin Amurka za su shiga cikin wannan runduna ta kasa da kasa ba.

XS
SM
MD
LG