Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obasanjo Na Nijeriya Ya Ce Zai Sake Nazarin Karin Farashin Mai... - 2003-06-30


Shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya ya yarda zai sake nazarin karin farashi mai yawa da aka yi wa mai a kasar, amma kungiyoyin kwadagon kasar sun ce wannan tayi nasa bai kai na janye yajin aikin da suke yi ba.

A bayan tattaunawar da bangarorin biyu suka yi a Abuja, babban birnin tarayya, shugaban kwadago na kasar, Adams Oshiomhole, ya ce koda yake sun yi marhabin da wannan tayi na shugaba Obasanjo, kungiyarsu ba zata daina yajin aiki ba har sai an janye karin farashin man.

Wannan mataki na shugaba Obasanjo ya kara farashin mai da kashi 54 daga cikin 100.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce shugaba Obasanjo zai kafa wani kwamiti wanda zai kunshi wakilan kwadago domin tattauna karin farashin man a ganawar da zasu yi nan gaba a yau litinin.

Babbar kungiyar kwadago ta Nijeriya, NLC, ta shirya yajin aiki na har sai illa ma sha Allahu, wanda aka fara yau litinin. Ma'aikata masu yawan gaske sun yi zamansu a gida, duk da umurnin da wata kotu ta bayar cewa yajin aikin haramun ne.

A Abuja da kuma Lagos, 'yan sandan kwantar da tarzoma sun yi ta harba barkonon tsohuwa a yayin da masu yajin aiki da kuma zanga-zanga suka kakkafa shingaye, suna kona tayu suna rera taken nuna kin jinin gwamnati.

An rufe kantuna da ofisoshi a dukkan biranen biyu, da kuma sauran manyan biranen kasar, ciki har da Kanon dabo, birni mafi girma a arewacin Nijeriya.

XS
SM
MD
LG