Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Yi Harbi Kan Masu Zanga-Zanga A Nijeriya - 2003-07-02


'Yan sanda a Nijeriya sun haddasa rudami yau laraba a Abuja, babban birnin kasar, a bayan da suka harba barkonon tsohuwa da harsasai na zahiri domin tarwatsa zanga-zangar nuna rashin yarda da karin farashin mai.

Mutane fiye da dubu daya suka ranta da gudu, a rude, a babbar kasuwar Abuja, a rana ta uku ta yajin aikin gama gari. Rahotanni sun ce mutane da dama sun ji rauni.

Haka kuma a yau laraba, 'yan sandan sun yi harbi da harsasai na zahiri a unguwanni da dama na Lagos, cibiyar kasuwancin kasar, domin tarwatsa 'yan zanga-zangar dake kokarin hana shiga kasuwanni.

Babbar kungiyar kwadago ta Nijeriya, NLC, ta zargi 'yan sanda da laifin nuna keta kan 'yan zanga-zangar da suka fara tayar da kayar baya ranar litinin, bayan da gwamnatin Olusegun Obasanjo ta yi karin farashin mai da sama da kashi 50 daga cikin 100.

Tun daga ranar da aka fara wannan yajin aiki, a kullum, 'yan sanda su kan yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zanga akasari a biranen Abuja da Lagos.

Haka kuma a yau laraba zanga-zanga ta yadu zuwa yankin kudu maso gabashin Nijeriya mai arzikin man fetur, inda masu zanga-zangar suka kunna wuta a kan manyan hanyoyin mota.

A can wani gefe kuwa, shugabannin kwadago sun zargi 'yan sanda da laifin harbewa tare da kashe kashe 'yan zanga-zanga hudu ranar litinin. Da farko wani kakakin 'yan sanda ya gaskata labarin kisar, amma kuma sai daga baya ya ce wai babu wani wanda ya rasa ransa dangane da wannan yajin aiki.

Shugabannin kwadago da gwamnati dai sun ci gaba da tattaunawa yau laraba domin cimma sasantawa kan karin farashin man. Shugaba Olusegun Obasanjo ya janye rangwamen farashin mai da ake yi, abinda ya sa farashinsa ya cilla sama da fiye da kashi 50 daga cikin 100.

XS
SM
MD
LG