Rundunar sojojin Uganda ta ce ta kwato yaran da 'yan tawayen arewacin kasar suka sace.
Kafofin labarai a Uganda sun ce yawan yaran da aka kwato ya kama daga 109 zuwa 249, amma kuma ba a tabbatar da wannan adadin ba.
An yi amannar cewa 'yan tawayen kungiyar "L.R.A." sun sace dubban yara da matasan Uganda tun lokacin da suka fara kokarin kifar da gwamnati a shekarar 1987. Ana tilastawa maza daga cikin yaran shiga aikin soja, yayin da ake tilastawa mata yin karuwanci.
Rundunar sojan Uganda ta ce an gano yaran a lokacin wani farmakin da aka kai kan 'yan tawayen kungiyar LRA a yankin arewa maso gabashin kasar.
A watan da ya shige, jami'an sojan Uganda sun ce 'yan tawayen sun sace 'yan mata akalla 30 lokacin da suka kai farmaki cikin wata makarantar sakandare kusa da garin Soroti a arewa maso gabashin kasar.