Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Yayi Alkawarin Goyon Bayan Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Na Afirka Ta Yamma A Liberiya - 2003-07-14


Shugaba Bush ya ce Amurka zata goyi bayan kokarin kasashen Afirka ta Yamma na kiyaye zaman lafiya a kasar Liberiya.

A bayan tattaunawar da yayi dazu da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, shugaban ya ce har yanzu yana nazarin irin rawar da ya dace Amurka ta taka a kasar ta Liberiya mai fama da yaki.

Amma kuma ya kara da cewa Amurka tana son tallafawa kungiyar kasuwar tattalin arzikin Afirka ta Yamma ta ECOWAS wajen ganin an samu cimma tsagaita wuta a Liberiya.

Mr. Kofi Annan ya ce su biyun sun cimma daidaiton ra'ayi kan yadda za a takali batun Liberiya, amma kuma bai yi karin bayani ba.

Mr. Bush ya ce idan an tura sojoji, zasu je ne kawai domin tabbatar da cewa ana yin aiki da shirin tsagaita wuta. Shugaban ya kara da cewa duk wani irin taimakon da Amurka zata bayar zai dogara ne a kan saukar shugaba Charles Taylor daga kan kujerar shugabancin Liberiya.

XS
SM
MD
LG