Bam ya ragargaza wata mota a babban birnin Iraqi kusa da wani ofishin hedkwatar rundunar sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya da kuma sabuwar majalisar mulkin Iraqi.
Kamfanonin dillancin labarun kasashen yammaci suka ce wannan al'amari ya faru a lokacin da wani mahari ya jefa gurneti cikin wurin ajiye motocin da 'yan jarida ke amfani da shi. Shaidu suka ce babu kowa a cikin motar da gurnetin ta fada kai, kuma babu rahoton jin rauni.
Tun da fari a yau litinin, an kashe sojan Amurka daya aka ji rauni ma wasu shida lokacin da aka kai hari kan kwambar motocinsu a tsakiyar birnin Bagadaza.
Hedkwatar sojojin Amurka ta ce an yi ta cilla gurneti kan motocin sojan na Amurka lokacin da aka yi musu kwanton-bauna a unguwar masu hannu da shuni ta Mansour.
An kashe sojojin Amurka su akalla 32 a hare-hare tun ranar daya ga watan mayu, lokacin da shugaba Bush ya ayyana karshen yaki gadan-gadan a Iraqi.