Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Powell Zai Gana Da Sanatoci Kan Batun Liberiya - 2003-07-16


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, zai gana da 'yan majalisar dattijai yau laraba domin tattauna yiwuwar tura sojojin Amurka zuwa Liberiya.

Amurka tana kara shan matsin lamba daga kasashen duniya a kan ta tura sojoji zuwa kasar ta Liberiya mai fama da yaki, inda a cikin 'yan kwanakin nan aka kashe daruruwan mutane, wasu dubbai suka rasa matsuguni a Monrovia, babban birnin kasar.

Shugaba Bush ya ce tana iya zamowa dole a tura sojojin Amurka zuwa kasar dake Afirka ta Yamma, amma kuma ya ce ba za a iya tura sojoji masu yawa ba, haka kuma ba za a iya barinsu a can na lokaci mai tsawo ba.

A jiya talata, babbar kungiyar 'yan tawayen Liberiya ta yi kira ga Amurka da ta tura sojojin da zasu iya karade kasar baki daya.

XS
SM
MD
LG