Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Sojan Amurka A Iraqi - 2003-07-16


Rundunar sojojin Amurka ta ce an kashe sojan Amurka daya aka raunata wasu guda uku yau laraba a lokacin da aka kai hari kan kwambar motocinsu a yammacin birnin Bagadaza.

jami'an soja sun fadawa Muryar Amurka cewa an bude wuta da kananan bindigogi da kuma gurneti kan kwambar motoci 30 na sojan Amurka.

A wani al'amarin dabam kuma, shaidu sun ce an raunata sojojin Amurka su akalla biyu, a lokacin da bam ya tashi ya ragargaza motarsu a kan wata hanya a wajen babban birnin na Iraqi.

Hare-haren sun zo a wannan rana ta cikar shekaru 24 da kwace mulkin da Saddam Hussein yayi a Iraqi.

Rundunar sojojin Amurka ta damu kan cewa magoya bayan Saddam zasu karrama wannan rana ta hanyar zafafa hare-haren da suke kaiwa sojojin Amurka.

XS
SM
MD
LG