Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Bai Wa Falasdinawa Agajin Kudi Dala Miliyan 20 - 2003-07-16


Amurka ta mikawa majalisar Mulkin kan Falasdinawa kudi dala miliyan 20 domin taimakawa wajen gyarawa da farfado da kayayyakin bukatun jama'a da suka lalace a sanadin watanni 33 da aka yi ana gwabzawa a tsakaninsu da Isra'ila.

A yau aka yi bukin mika wannan kudi, wanda shine karon farko da Amurka ta bayar da agajin kudi kai tsaye ga Falasdinawa.

A can baya, Amurka tana bayar da agaji ga Falasdinawa ne ta hannun kungiyoyi na kasa da kasa, amma a cikin 'yan kwanakin nan gwamnatin Mr. Bush ta bayyana amincewarta da firayim ministan Falasdinawa Mahmoud Abbas.

Mr. Abbas ya ce nan gaba cikin wannan watan zai gana da shugaba Bush a nan Washington.

A halin da ake ciki, firayim ministan Bani Isra'ila Ariel Sharon ya yada zango a Norway domin tattauna shirin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da takwaransa na kasar, Kjell Magne Bondevik.

XS
SM
MD
LG