Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush Da Blair Sun Kare Shawararsu Ta Abka Ma Iraqi Da Yaki - 2003-07-18


Shugaba Bush da firayim minista Tony Blair na Britaniya sun kare shawarar da suka yanke ta kai farmaki kan kasar Iraqi, suna masu fadin cewa za a gano gaskiyar ikirarinsu game da muggan makaman Saddam Hussein.

A lokacin da suke ganawa da 'yan jarida jiya alhamis a fadar White House, shugabannin biyu sun yi watsi da zargin da ake yi cewar har yanzu ba a gano wani makamin kare-dangi a Iraqi ba, da kuma gardamar da ake yi a yanzu cewar bayanin leken asirin da suka yi amfani da shi wajen kai harin ba ya da tushe.

Shugaba Bush ya ce gano irin wadannan makamai zai kawo karshen abinda ya kira "gardamar" da ake yi kan an dauki matakin soja bisa Iraqi ba tare da hujja ta gari ba.

Mr. Blair ya ce babu wani shugaban kwarai da zai yi watsi da shaidar cewa makaman kare-dangi na Iraqi suna yin barazana ga duniya.

XS
SM
MD
LG