Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Gocewa Da Fada A Liberiya - 2003-07-18


Fada ya sake barkewa a kasar Liberiya, a bayan da sojojin 'yan tawaye da na gwamnati suka fara kece raini a wajen Monrovia, babban birnin kasar.

'Yan tawayen suna wani wuri mai tazarar kilomita 20 daga tsakiyar birnin na Monrovia. Gwamnatin Liberiya ta zarge su da laifin kai sabon farmaki kan Monrovia, amma 'yan tawayen suka ce suna kare yankunan da tuni ke hannunsu ne.

Wannan fada na baya-bayan nan ya janyo fargabar cewa shirin tsagaita wuta maras karko da ake aiki da shi tsakanin sassan biyu masu gaba da juna yana iya wargajewa.

A jiya alhamis, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Liberiya, Jacques Klein, ya ce Amurka tana da niyyar tsoma hannu ne kawai a bayan an girka sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka ta Yamma.

Kungiyar Tarayyar Tattalin Arzikin Afirka ta yamma ta ECOWAS ta yi alkawarin tura ayarin farko na sojojin kiyaye zaman lafiya su akalla dubu daya, amma kuma ba a sa ran cewa zasu isa can sai watan Agusta.

XS
SM
MD
LG