Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jaridun Isra'ila Sun Ce Firayim Minista Sharon Yana Tunanin Sako Falasdinawa Fursunoni - 2003-07-18


Jaridun Isra'ila sun ce firayim minista Ariel Sharon yana nazarin sakin wasu fursunonin Falasdinawa, ciki har da 'ya'yan kungiyoyin kishin Falasdinu na "Islamic Jihad" da "Hamas."

Rahotannin da jaridun suka buga yau Jumma'a sun ce Mr. Sharon yana tunanin sakin 'yan kishin Falasdinu har 60 wadanda ba a same su da hannu a hare-haren ta'addanci kan Isra'ila ba.

Sakin wadannan fursunoni zai zamo wani matakin nuna fatar alheri kafin tattaunawar da Mr. Sharon zai yi jibi lahadi da firayim ministan Falasdinawa, Mahmoud Abbas.

Malam Abbas ya bukaci da a sako dukkan Falasdinawan dake kurkuku, koda yake ba a ambaci wannan batu kai tsaye ba a cikin shirin da aka gabatar na cimma zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

XS
SM
MD
LG