Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Ki Yarda Da Jinkirta Shari'ar Foday Sankoh A Saliyo - 2003-07-23


Kotun bin kadin laifuffukan yaki da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa a Saliyo, ta ki yarda da bukatar da aka gabatar mata, ta jinkirta shari'ar tsohon madugun 'yan tawaye Foday Sankoh bisa dalilai na rashin lafiya.

Lauyoyin Mr. Sankoh sun ce tsohon madugun 'yan tawayen, wanda ake zargin kungiyarsa ta "Revolutionary United Front" da laifin tsananin mugunta, ba ya da cikakkiyar lafiyar da zai iya tsayawa gaban shari'a.

Har ila yau wannan kotu ta ki yarda da irin wannan rokon da wani kwamandan 'yan tawaye mai suna Alex Brima shi ma yayi mata. Kotun ta ki yarda ta bayar da belin Mr. Brima.

XS
SM
MD
LG