Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ci Gaba da Gwabza Fada A Kasar Liberiya - 2003-07-23


An ci gaba da luguden wuta tare da harbe-harbe jefi-jefi a rana ta biyar a jere a Monrovia, babban birnin Liberiya, duk da kiran da aka yi na tsagaita wuta.

An ci gaba da fada yau laraba, duk da rahoton da aka buga cewa shugaba Charles Taylor yana shirin sauka cikin kwanaki goma.

Jaridar New York Times ta ambaci Mr. Taylor yana fadi cikin hirar da ta yi da shi ta wayar tarho cewar ya yanke shawarar zai mikawa kakakin majalisar wakilai mulkin kasar. Jaridar ta ambaci Mr. Taylor yana fadin cewa yana da niyyar bayar da sanarwar haka nan ba da jimawa ba.

A halin da ake ciki, batun tsagaita wuta ya zamo daya daga cikin sharrudan tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasar wadda yaki ya lalata, wadda kuma 'yantattun bayi daga nan Amurka suka kafa a tsakiyar karni na 19.

Ministocin tsaron kasashen Afirka ta yamma sun gana a Senegal domin tsara yawa da lokacin girkawa da kuma bukatun rundunar share fage ta 'yan kiyaye zaman lafiya da za a tura can.

Amma kuma shugabannin yankin sun bayyana a fili cewa ba za a tura sojojin ba har sai an cimma zaman lafiya da zasu je su kiyaye.

XS
SM
MD
LG