Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hambararren Shugaban Sao Tome Ya Koma Gida... - 2003-07-23


Shugaban tarayyar tsibiran Sao Tome da Principe ya koma wannan karamar kasa dake Afirka ta Yamma, mako guda a bayan da sojoji suka hambarar da shi a wani juyin mulkin da babu zubar da jini.

Shugaba Fradique de Menezes ya sauka a tsibirin dazu da maraice, jim kadan a bayan da wani babban mai shiga tsakani ya bayar da sanarwar cimma yarjejeniyar mayar da zababben shugaban bisa kan kujerarsa.

Tun da fari, ministan harkokin wajen Gabon, Jean Ping, ya shaidawa 'yan jarida cewa shugaba Menezes da shugabannin 'yan juyin mulki sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar maido da yin aiki da tsarin mulki a Sao Tome.

A karkashin yarjejeniyar, majalisar dokokin tarayyar zata gana domin jefa kuri'a kan kudurin yin ahuwa ga wadanda ke da hannu a juyin mulkin.

XS
SM
MD
LG