Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Kanjamau Ta AIDS Tana Barazana Ga Tattalin Arzikin Kasashen Afirka - 2003-07-23


Wani sabon nazari na Bankin Duniya yayi kashedin cewa cutar kanjamau ta AIDS, ko SIDA, da kuma kwayar halittar HIV mai haddasa ta, zasu iya illa fiye da yadda aka zata tun farko ga tattalin arzikin kasashen Afirka.

Rahoton da aka bayar a yau laraba ya ce kasashen da suka fi fama da cutar kanjamau ta AIDS a Afirka zasu iya hasarar fiye da rabin yawan kayayyakin da kasashensu ke sarrafawa a cikin shekaru casa'in (90) masu zuwa.

Nazarin ya nuna cewa akasarin masu mutuwa daga cutar kanjamau matasa ne, abinda ke janyo marayu masu yawan gaske.

Nazarin ya ce da wuya marayun da iyayensu suka mutu a sanadin cutar kanjamau su kammala karatu har su zamo masu ilmin da zasu tabuka wani abu a kasa.

Nazarin ya bayar da shawarar daukar matakan gaggawa na tsawaita rayukan masu fama da cutar ta yadda zasu iya kulawa da 'ya'yansu tare da ilmantar da su.

XS
SM
MD
LG