Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ce Ba Ta tababar Mutuwar Qusay Da Uday, 'Ya'yan Saddam Hussein - 2003-07-23


Babban kwamandan sojojin Amurka a Iraqi, ya ce babu shakka ko miskala zarratin sojojin Amurka sun kashe 'ya'yan saddam Hussein maza, Qusay da Uday.

Janar Ricardo Sanchez ya ce wasu jami'an hambararriyar gwamnatin Iraqi su hudu sun tabbatar da gawar 'yan'uwan a bayan farmakin da sojojin Amurka suka kashe su a wani gida dake birnin Mosul.

Janar Sanchez ya ce sannu kan hankali jami'an Amurka zasu gabatar da shaidar mutuwar yaran biyu. Jami'an ma'aikatar tsaro sun ce gwamnatin Mr. Bush tana muhawara a kan ko ta rarraba hotunan gawarwakin 'yan'uwan biyu ko a'a.

Jami'an suka ce hotunan ba su da kyaun gani, amma kuma watakila raba su zata tabbatarwa da al'ummar Iraqi cewa da gaske ne an kashe Qusay da Uday.

A halin da ake ciki, wani gidan telebijin na larabci ya watsa wani kaset dauke da muryar da aka ce ta hambararren shugaban Iraqi ne, Saddam Hussein.

A yau laraba gidan telebijin na al-Arabiyya ya watsa wannan kaset, kwana daya a bayan da sojojin Amurka suka kashe 'ya'yan Saddam maza biyu a Mosul.

Muryar dake kan wannan kaset ta yi kira ga sojojin Iraqi da su tashi su yaki sojojin taron dangi, tana mai cewa har yanzu ba a kare yaki a Iraqi ba.

babu waata hanyar da za a iya hakkake sahihancin muryar dake kan wannan kaset cikin lokaci kankani. Amma kuma tsohon jakadan Iraqi a Majalisar Dinkin Duniya ya ce babu shakka wannan murya ta Saddam Hussein ce.

XS
SM
MD
LG