Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Abubuwa Matafiyi Ke Iya Shiga Amurka Da Su? - 2003-07-28


1. Babu ka'idar yawan kudin da mutum matafiyi zai iya shiga da shi Amurka. Amma kuma idan har mutum yana dauke da kudi (tsabar kudi, ko ceki, ko mani-oda da sauransu) wanda ya zarce dala dubu goma ($10,000), to tilas ne ya bayyanawa jami'in kwastam. Idan kuwa mutum bai bayyana ba, kuma aka samu wannan kudi a jikinsa, to za a iya kwacewa. Idan matafiya biyu ko fiye da haka (masu tafiya tare, misali mace da mijinta) suka cika takardar bayyana kudin tare, to tilas su bayyana adadin da dukkansu ke dauke da shi. Ba a bukatar mutum ya bayyana yawan kudin dake jikin katin bashi.

2. Kowane maziyarci zai iya shiga Amurka da tsarabar da ba ta zarce ta dala dari daya ba ($100), kuma ba tare da ya biya kudin kwastam ba. Idan tsarabar ta zarce haka har zuwa dala dubu daya, za a biya kudin kwastam na kashi uku daga cikin dari (3%).

3. Ya kamata matafiyi ya san cewa ana iya neman mutum ya biya kudin kwastam a kan kayayyakin da aka saye su a kantunan da ba a biyan haraji na filayen jiragen sama ko a filayen jiragen. A takaice, a kan bukaci mutum ya biya kudin kwastam a kan barasar da ta shige lita daya, ko taba sigarin da ta shige kwaya 200.

4. Tilas matafiyi ya bayyanawa jami'in kwastam idan yana dauke da kayan abinci, kowane iri ne. A kan kyale mutum ya shige da kayayyakin abinci dabam-dabam, kamar su goro, ko yaji ko kuka da makamantansu, amma kuma tilas ne a bincika su domin tabbatar da cewa ba su dauke da cuta ko tsutsa. Alal misali, idan aka samu goro guda daya da tsutsa, to ana kwace sauran goron baki daya a zubar. Idan mutum bai bayyana cewa yana dauke da kayan abinci ba, aka kuma samu a wurinsa, to za a kwace a zubar, sannan zai biya tara.

5. An haramta shiga Amurka da irin tabar nan da ake kira "Cigar" 'yar kasar Cuba, ko kayayyakin da suka samo asali daga Cuba. Idan kana da wani abu wanda aka kera a Cuba, ko ya samo asali daga kasar, to ka bar shi a gida, domin lallai za a kwace.

Allah Ya kiyaye hanya, ya bayar da sa'ar tafiya, amin summa amin.

XS
SM
MD
LG