Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Foday Sankoh Ya Mutu - 2003-07-30


Tsohon madugun 'yan tawayen Saliyo, wanda aka tuhuma da aikata laifuffukan yaki, Foday Sankoh, ya mutu, a bayan da ya jima yana laulayi.

An bayyana mutuwar tasa a cikin wata sanarwar da ta fito daga hannun kotun bin kadin laifuffukan yaki ta MDD a Saliyo, wadda take tsare da Mr. sankoh tana tuhumarsa da cin zarafin bil Adama.

Kotun ta ce jiya da daddare Mr. Sankoh ya mutu a wani asibitin birnin Freetown. An yi imanin cewa yana da shekaru sittin da wani abu.

Foday Sankoh shine ya kafa kungiyar 'yan tawayen "Revolutionary United Front" wadda ta fara tayar da kayar baya a shekarar 1991.

Sojojinsa sun yi kaurin suna wajen nuna tsananin mugunta, kamar fyade da kuma datse hannaye da kafafuwa da kunnuwa da hancin fararen hula da yara kanana.

A cikin sanarwar da ta bayar a yau, kotun ta ce mutuwar Mr. Sankoh ba zata hana ta bin kadin hannun da yake da shi a cikin abinda ta kira "munanan ayyukan ta'asa" ba.

An jefa Mr. Sankoh a kurkuku tun watan mayun shekara ta 2000, aka kuma mika shi hannun wannan kotun a watan Maris da ya shige.

XS
SM
MD
LG