Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Ce Har Yanzu Ana Iya Kafa Kasar Falasdinu A Shekarar 2005 - 2003-07-30


Shugaba Bush ya ce har yanzu ana iya cimma burin kafa kasar Falasdinu nan da shekara ta 2005.

A lokacin da yake magana da 'yan jarida yau laraba a fadar White House, Mr. Bush ya ce yana tsammanin ana samun ci gaba sosai a shiga tsakanin da ake yi a rikicin Isra'ila da Falasdinawa.

Ya bayyana kwarin guiwarsa kan firayim ministocin sassan biyu, wadanda duka suka ziyarci fadar White House cikin mako gudan da ya shige.

A halin da ake ciki dai, ana sa ran manyan jami'an tsaron Isra'ila da na Falasdinawa zasu gana yau laraba domin tattauna janye wasu daga cikin sojojin Isra'ila daga wasu garuruwan Falasdinawa guda biyu, watakila garuruwan Qalqilyah da Jericho a yankin Yammacin kogin Jordan.

XS
SM
MD
LG