Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Kece Raini A Wasu Birane Biyu A Kasar Liberiya - 2003-07-30


An sake ci gaba da gwabza kazamin fada yau laraba a birane biyu da suka fi girma a kasar Liberiya, duk da sake kiran da shugabannin 'yan tawaye suka yi na a tsagaita wuta.

Sojojin gwamnatin shugaba Charles Taylor suna gwabzawa domin kare Monrovia, babban birnin kasar, da kuma birni na biyu wajen girma a kasar, Buchanan, daga wasu kungiyoyin 'yan tawaye biyu da suka dukufa a kan sai sun tumbuke Mr. Taylor daga kan kujerar shugabancin kasar.

Dakarun babbar kungiyar 'yan tawayen kasar sun yi kokarin tsallaka wasu gadoji domin shiga tsakiyar birnin Monrovia a yau laraba, kwana guda a bayan da shugabanninsu suka yi alkawarin daina fada tare da janyewa zuwa bakin tashar jiragen ruwan birnin domin jiran isar sojojin kiyaye zaman lafiyar da aka yi alkawarin turawa.

Sojojin Mr. Taylor kuma sun kasa kwato birnin Buchanan, kwana guda a bayan da karamar kungiyar 'yan tawayen kasar da ake kira "MODEL" ta kwace shi.

A yayin da ake ci gaba da bai wa hammata iska a can kuma, kungiyar Kasuwar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, ta fara kusantar tura sojojin kiyaye zaman lafiya. Wani janar na sojojin Nijeriya wanda zai jagoranci ayarin farko na 'yan kiyaye zaman lafiya dubu daya da dari biyar, ya tafi Liberiya domin auna irin bukatunsu.

XS
SM
MD
LG