Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Mulkin Da Amurka Ta Kafa A Iraqi Ta Nada Shugabanta Na farko - 2003-07-30


Majalisar mulkin da Amurka ta kafa a kasar Iraqi, ta zabi shugabanta na farko.

Ibrahim al-jafari, daya daga cikin shugabannin jam'iyyar Dawa mai kishin addinin Islama, zai rike wannan mukamin shugaba na karba-in-karba a watan agusta.

A jiya talata majalisar mai wakilai 25 ta yanke shawarar gudanar da mulkin karba-in-karba a tsakanin wasu membobinta guda 9, a bayan da ta kasa yarda da shugaba guda daya tak.

Ana amfani da farkon haruffan sunayen mutanen wajen zaben wadanda zasu fara hawa kan wannan kujera.

A halin da ake ciki, hukumar leken asirin Amurka ta CIA ta ce ta yi imani da cewa muryar Saddam Hussein ce aka ji a jikin wani kaset na baya-bayan nan da wani gidan telebijin na larabci ya watsa.

Sojojin Amurka sun dukufa wajen farautar hambararren shugaban na Iraqi.

XS
SM
MD
LG