Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Liberiya Dake Rawar Murna Sun Tarbi Sojojin Nijeriya - 2003-08-04


Sojojin Nijeriya sun fara isa Liberiya, a matakin farko na aikin zaman lafiyar da za a gudanar da nufin tabbatar da zaman lafiya a wannan kasa da yaki ya lalata.

Ayarin farko na sojojin kiyaye zaman lafiyar sun yi ta sauka duk tsawon rana yau litinin a babban filin jirgin saman Robertsfield International dake Monrovia, babban birnin Liberiya.

Duk da ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ta zubawa, daruruwan 'yan Liberiya sun fito suka tarbi sojojin. Fararen hular dake rera waka suna fadin cewa yaki ya kare, sun dauki wani sojan Nijeriya a ka suna yawo da shi.

Za a girka sojoji fiye da dubu uku a wannan aikin kiyaye zaman lafiyar da kungiyar ECOWAS zata gudanar. A bayan Nijeriya, rundunar zata hada da sojoji daga kasashen Ghana da Mali da Benin da kuma Togo. A watan Oktoba wata babbar kungiyar kiyaye zaman lafiyar ta Majalisar Dinkin Duniya zata maye gurbin wannan.

Aikin da sojojin zasu yi shine na tabbatar da cewa ana yin aiki da shirin tsagaita wuta, tare da samar da sukunin rarraba kayan agaji.

Gwamnatin Liberiya da 'yan tawaye masu yin gaba da ita duk sun yi marhabin da saukar ayarin farko na sojojin kiyaye zaman lafiyar. Babbar kungiyar 'yan tawayen Liberiya ta LURD ta ce zata janye daga Monrovia da zarar sojojin kiyaye zaman lafiya sun shiga birnin.

XS
SM
MD
LG