Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubbai Sun Fito Domin Murna A Lokacin Da Sojojin Nijeriya Suka Ratsa Cikin Birnin Monrovia - 2003-08-07


Sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka ta yamma sun shiga cikin Monrovia, babban birnin Liberiya da yaki ya lalata a karon farko, inda dubban fararen hula dake murna suka fito domin yi musu marhabin.

Mutane sun yi jerin gwano a gefen tituna wasu da kyalle suna furta cewa, "babu sauran yaki, zaman lafiya muke so," a yayin da sojojin suke shiga cikin wannan birni.

Sojojin Nijeriya su 450 sun fara isa Liberiya a ranar litinin, a zaman ayarin farko na sojojin da yawansu zai kai dubu 3 da 200. Sojojin sun yi sansani a babban filin jirgin sama, mai tazarar kilomita 45 daga birnin na Liberiya.

A wani labarin, shugaba Charles Taylor na Liberiya ya kara nanata alkawarin da yayi na yin murabus ranar litinin, yana mai cewa zai mika mulki ga mataimakin shugaba Moses Blah. A cikin hirar da yayi da gidan telebijin na CNN, Mr. Taylor ya ce zai yi jawabi ga al'ummar kasarsa ranar lahadi.

A wani zaman gaggawa da ta yi yau alhamis a Monrovia, majalisar dokokin Liberiya ta amince da shawarar Mr. Taylor ta sauka tare da mika mulki ga mataimakin shugaban.

Shugaba Taylor yayi na'am da mafakar da Nijeriya ta ba shi, amma kuma bai ce ga lokacin da zai bar Liberiya ba. Gwamnatin shugaba Bush ta nan Amurka ta sha yin kira ga Mr. Taylor da ya sauka ya bar Liberiya domin a samu zaman lafiya a kasar.

XS
SM
MD
LG