Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 11 Sun Mutu A Harin Bam Da Aka Dana Cikin Mota A Bagadaza - 2003-08-07


Mutane 11 sun mutu, wasu masu yawa sun ji rauni a lokacin da wani bam da aka dana cikin mota ya tashi a kofar ofishin jakadancin kasar Jordan dake Bagadaza.

Wani jami'in 'yan sanda na Iraqi ya ce akwai 'yan sandan Iraqi su biyar dake aikin gadi a ofishin jakadancin cikin mutanen da suka mutu.

Wannan bam ya lalata ginin ofishin sosai, ya kuma raunata wasu ma'aikata biyar.

Jordan ta bukaci Amurka da ta kara matakan tsaro a ofishin jakadancin na Jordan.

Wani jami'in ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, ya ce 'yan sandan Iraqi ne ba wai sojojin kawance ba zasu ringa gadin ofisoshin jakadancin kasashen waje.

Haka kuma, a yau alhamis sojojin Amurka biyu sun ji rauni a lokacin da aka bude wuta kan motarsu a kan wani titin Bagadaza dake shake da kantuna.

XS
SM
MD
LG