Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Litinin Za A Koma Ga Shawarwarin Neman Zaman Lafiya A Sudan - 2003-08-11


Yau litinin a kasar Kenya, gwamnatin Sudan da 'yan tawayen kudancin kasar zasu koma kan teburin shawarwari a ci gaba da kokarin kawo karshen yakin basasar shekaru 20 a kasar.

Jiya lahadi aka shirya fara ci gaba da tattaunawa, amma kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce an jinkirta a bayan da jami'in kasar Kenya mai shiga tsakani ya fuskanci jinkirin zuwa wurin babu zato babu tsammani.

Jami'an Sudan da na 'yan tawayen kudanci sun yarda zasu ci gaba da tattaunawar, duk da sabanin ra'ayin da suke da shi dangane da daftarin zaman lafiyar da masu shiga tsakani na yankin suka gabatar a watan da ya shige.

Gwamnatin Sudan dai ta ce ba ta yarda da wannan daftarin yarjejeniya ba, tana mai bayyana shi a zaman matakin farko na ballewar yankin kudancin Sudan.

XS
SM
MD
LG