Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Sa Ran Karin Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Zasu Isa Liberiya - 2003-08-15


Sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka ta Yamma dake Monrovia, babban birnin Liberiya, suna zaman jiran karin abokan aiki, yayin da shugaban rikon kwarya na Liberiya, Moses Blah, yake tattaunawa da shugabannin 'yan tawaye a Ghana.

Ana sa ran karin sojojin Nijeriya su 800 zasu isa Liberiya nan da gobe, matakin da zai ninka yawan sojojin wannan runduna ta ECOMIL da yanzu ke kasar. Wasu sojojin kundumbalar Amurka su 200 suna can Liberiyar domin taimakawa wajen tsare tashar jiragen ruwan Monrovia, ta yadda jiragen dake dauke da abinci na agaji zasu iya shiga ciki.

A jiya alhamis, sojojin kiyaye zaman lafiyar sun shiga cikin yankin dake hannun 'yan tawaye suka amshi ikon kula da tashar jiragen ruwan. 'Yan tawaye sun mika tashar jiragen ruwan a wani gajeren bukin da aka yi a kan gadar da ta hada yankunansu da yankunan da gwamnati ke rike da su a Monrovia.

Jakadan Amurka a Liberiya, John Blaney, da kwamandan rundunar kiyaye zaman lafiya ta ECOMIL, janar Festus Okonkwo, suna wurin a lokacin da 'yan tawaye suka janye daga tashar ta Freeport. Dubban fararen hula sun makare kowane gefen gadar domin kallon wannan buki.

Har ila yau a jiya alhamis, shugaban rikon kwarya Moses Blah, ya fara tattaunawar neman zaman lafiya a kasar Ghana da wakilan kungiyoyin 'yan tawayen Liberiya biyu, LURD da MODEL. Tattaunawa tsakanin bangarorin ta cije makonnin da suka shige a lokacin da ake gwabza fada mafi muni a ciki da kewayen babban birnin Liberiya.

XS
SM
MD
LG