Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Na Nijeriya Sun Isa Liberiya - 2003-08-17


Ayari na biyu na sojojin kiyaye zaman lafiya 'yan Nijeriya sun isa Monrovia, babban birnin Liberiya, a yayin da aka kasa cimma tazara a tattaunawar siyasa da ake yi a tsakanin shugaban rikon-kwarya Moses Blah da shugabannin 'yan tawaye a Ghana.

Sojojin na Nijeriya su 110 sun isa Monrovia jiya asabar, abinda ya kawo adadin sojojin kiyaye zaman lafiyar dake Liberiya a yanzu zuwa kusan dubu daya.

ma'aikatan agaji a babban birnin na Liberiya sun yi rokon da a taimaka musu da kayan aiki domin rarraba kayan abinci da magungunan da ake matukar bukata a cikin birnin.

A can kasar Ghana kuwa, shugaban rikon kwarya Moses Blah ya tattauna da shugabannin 'yan tawaye jiya asabar kan batun kafa gwamnatin rikon kwarya idan ya sauka a cikin watan Oktoba, amma babu wani ci gaban da aka samu.

Rahotanni sun ce 'yan tawayen sun bukaci da a ba su manyan mukamai ciki har da kujerar mataimakin shugaban kasa da ta kakakin majalisar dokoki.

XS
SM
MD
LG