Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Burundi Zai Gana Da Madugun Babbar Kungiyar 'Yan Tawayen Kasar - 2003-08-18


Shugaba Domitien Ndayizeye na kasar Burundi zai gana gobe talata da madugun babbar kungiyar 'yan tawayen kasar a Pretoria, babban birnin Afirka ta Kudu.

Jami'an Burundi sun ce tattaunawar zata mayar da hankali ga shirye-shiryen raba ikon mulki a tsakanin sassan kasar masu gaba da juna. Wannan ganawa ta su ta zo a daidai lokacin da kasashen yankin suke shirin gudanar da wani taron koli kan Burundi daga ranar 24 ga wannan wata na Agusta.

A wani taron koli na yankin da aka gudanar a watan jiya, gwamnatin Burundi da kungiyar 'yan tawayen mai suna "Dakarun Kare Dimokuradiyya" sun yarda zasu yi aiki da shirin tsagaita wutar da kusan an yi watsi da shi.

Kungiyoyin 'yan tawayen kabilar Hutu da dama sun shekaru goma suna yakar rundunar sojojin kasar wadda 'yan kabilar Tutsi suka kanainaye. An yi kiyasin cewa an kashe mutane dubu 300 a wannan tashin hankalin.

XS
SM
MD
LG