Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kwantar Da Wutar Fitina A Warri - 2003-08-22


Sojoji masu yawa da aka girka a garin Warri na yankin hakar mai a kudancin Nijeriya, sun kwantar da wutar fitina, a bayan da aka yi kwana da kwanaki ana gwabza fadan kabilanci.

Daruruwan sojoji sun shiga garin ranar laraba suka fara yin sintiri a kan tituna.

Shi ma gwamna James Ibori na Jihar Delta ya isa garin na warri ranar laraba domin yayi kokarin warware wannan rikici. A bayan da ya gana da wakilan kabilun Ijaw da Itsekiri masu gaba da juna, ya ce sassan biyu sun yarda za su daina bude wuta haka.

Kabilun Ijaw da Itsekiri sun jima suna tsama da juna domin neman fifiko a fagen siyasa da na tattalin arziki a wannan yanki mai arzikin mai. Musamman 'yan kabilar Ijaw suna gaba da gwamnatin Nijeriya wadda suka ce tana fifita 'yan kabilar Itsekiri.

Shugaba Olusegun Obasanjo ya roki dukkan sassan da kada su yi amfani da wannan rikici wajen satar mai daga bututun man da ya ratsa ta cikin yankin nasu. A kai a kai, mazauna yankin sukan fasa wannan bututu domin satar man da ake turawa ta ciki.

XS
SM
MD
LG