Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilan Da Suka Halarci Taron Neman Zaman Lafiyar Liberiya Sun Tsallake Rijiya Da Baya - 2003-08-22


Wakilan dake komawa gida daga taron neman zaman lafiya a Liberiya da aka gudanar a Accra, babban birnin Ghana, sun jijjiga jiya alhamis, kuma cikinsu ya dura ruwa, a bayan da tayar jirginsu ta karye lokacin da suke kokarin tashi daga babban filin jirgin saman Accra, a kasar Ghana.

Wannan lamari ya sa jirgin yayi ta zamiya kan tumbinsa a hanyar tashin jirgin. Akwai fasinjoji 44 ciki har da wakilan 'yan tawaye da na gwamnati a cikin wannan jirgi.

Wakilan suna kan hanyarsu ta komawa gida ne a bayan tattaunawar kwanaki 78 da ta kai ga zaben da aka yi wa Gyude Bryant a zaman shugaban rikon kwarya.

Ba a san abinda ya janyo karyewar tayar wannan jirgi ba. Babu kuma wani wanda ya ji mummunan rauni a wannan hadarin.

XS
SM
MD
LG