Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gawa Ta Mike! - 2003-08-23


Wani tsoho dan kasar Vietnam da aka dauka ya mutu, ya mike a bayan da ya shafe sa'o'i da dama cikin dakin ajiye gawarwaki na wani asibitin birnin Ho Chi Minh.

Jami'an lafiya suka ce 'yan'uwan Nguyen Van Quan mai shekaru 73 da haihuwa sun same shi da ransa a lokacin da suka je dauko gawarsa domin binnewa.

An kwantar da wannan tsoho a asibitin mako gudan da ya shige, a bayan da ya koka da ciwon kirji. Zuciyarsa ta daina bugawa, saboda haka a ranar Jumma'a sai likitoci suka ce ya mutu, sai kuma aka kai shi dakin ajiye gawarwaki.

Sa'o'i da dama bayan da aka ce ya mutu, sai 'yarsa da mijinta suka zo daukar gawar. Sun firgita a lokacin da suka ga kyallen da aka rufe shi da shi yana motsi. 'Yar ta shaidawa 'yan jarida cewar a lokacin da ma'aikatan dakin ajiye gawarwakin suka garzayo suka bude wannan kyalle, sai suka ga ashe idanunsu biyu, kuma da ganin 'yar tasa da mijinta sai ya fara murmushin murna.

Rahoton karshe da aka samu dai ya ce Mr. Quan yana kwance har yanzu a asibiti, yayin da aka fara binciken yadda lamarin ya kasance haka.

XS
SM
MD
LG