'Yan Rwanda za su kwarara zuwa rumfunan zabe ranar litinin domin zaben shugaban kasa na farko da za a gudanar tun bayan kashe-kashen kare-dangi na 1994, lokacin da a cikin wa'adin watanni uku, 'yan tsageran kabilar Hutu suka hallaka mutanen da aka ce sun kai dubu 800 'yan kabilar Tutsi da 'yan kabilarsu at Hutu masu sassaucin ra'ayi.
Ana sa ran cewa shugaban kasar na yanzu dan kabilar Tutsi, Paul Kagame, zai lashe wannan zabe cikin ruwan sanyi. Mr. Kagame shine ke mulkin kasar tun lokacin da sojojinsa 'yan tawaye suka kawo karshen kashe-kashen.
Babban abokin takararsa shine Faustin Twagiramungu, tsohon firayim minista kuma dan kabilar Hutu mai sassaucin ra'ayi. Mr. Twagiramungu ya fito a fili yana sukar gwamnatin Mr. Kagame wadda ya bayyana a zaman ta kama-karya.
A jiya jumma'a, kungiyar kare hakkin bil Adama ta "Amnesty International" ta zargi gwamnatin Rwanda da laifin shirya wannan zabe cikin yanayi na tsoratarwa da cin zarafin jama'a.