Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Amurka Sun Ce Libya Ta Kammala Zuba Dala Miliyan Dubu Biyu Da 700 Cikin Wani Asusu - 2003-08-23


Jami'an Amurka sun ce Libya ta zuba kudi dala miliyan dubu 2 da 700 cikin asusu a wani bankin kasar Switzerland domin biyan diyya ga iyalan mutanen da suka mutu a harin bam na Lockerbie a 1988.

Ta hanyar zuba kudi cikin wannan asusu, a yanzu Libya ta cika alkawuran da ta dauka a karkashin yarjejeniyar da aka kulla a makon da ya shige, ta kuma share fagen dage takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya mata.

Haka kuma a jiya Jumma'a, Faransa ta ce watakila nan ba da jimawa ba za a cimma yarjejeniya tsakaninta da Libya kan yawan diyyar da za a biya iyalan mutanen da suka mutu a harin bam da aka kai kan wani jirgin saman Faransa a 1989.

Wannan sanarwa ta zo kwana guda a bayan da Faransa da Ingila suka yarda za su jinkirta jefa kuri'a a zauren Kwamitin Sulhun MDD kan dage takunkumin da aka sanyawa Libya.

Wannan jinkirin zai bai wa Faransa damar sake tattauna yawan diyyar da za a biya iyalan mutane 170 da suka mutu a harin bam da aka kai kan jirgin kamfanin UTA wanda ya tarwatse a samaniyar Jamhuriyar Nijar a 1989.

Libya ta biya diyyar dala miliyan 33 ne kacal ga iyalan mutanen, yayin da ta yarda za ta biya diyyar dala miliyan dubu 2 da 700 ga iyalan mutane 270 da suka mutu a harin na Lockerbie wadanda yawancinsu Amurkawa ne.

Faransa ta ce tsananin bambancin dake tsakanin yawan diyyar da za a biya nata iyalan da na Lockerbie cin mutunci ne ga Faransawa.

XS
SM
MD
LG