Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Ce Zata Ci Gaba Da Kashe Shugabannin Kungiyoyin Kishin Falasdinu. - 2003-08-23


Isra'ila ta lashi takobin cewa zata kashe wasu shugabannin kungiyoyin masu zazzafan kishin Falasdinu, duk da kururuwar daukar fansar da dubban Falasdinawa dake jana'izar wani shugaban Hamas da Isra'ila ta kashe suka yi.

Zaman tankiya ta karu jiya Jumma'a lokacin ad sojojin Isra'ila suka kashe wani dan kishin Falasdinu guda da aka rutsa da shi a cikin wani asibiti a yankin Yammacin kogin Jordan.

Gidan telebijin na Isra'ila kuma ya ce an girka tankoki da sojoji masu yawa a bakin iyakar zirin Gaza, su na jiran umurnin shiga cikin yankunan Falasdinawa.

Wani jirgin saman helkwafta na sojan Isra'ila ya cilla makamai masu linzami ya kashe wani jagoran kungiyar Hamas, Isma'il Abu Shanab, a bayan da hamas ta kai harin kunar bakin wake cikin wata motar safa ranar talata a al-Qudus, ta kashe mutane 20.

Shugaba Bush na Amurka ya ce tilas ne Falasdinawa su rushe kungiyoyin masu zazzafan kishi dake kai hare-hare kan Isra'ila idan har suna son samun kasarsu 'yantacciya a karkashin shirin da Amurka ta tsara na cimma zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG