Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nuna Amurkawan Da 'Yan Tawayen Colombia Ke Rike Da Su A Hoton Bidiyo - 2003-08-29


Jami'an Amurka sun ce wani faifan bidiyo da aka samo ya zanmo shaidar farko da aka gani cewa wasu Amurkawa masu aikin kwangila na ma'aikatar tsaron Amurka da 'yan tawaye suka sace cikin watan Fabrairu a kasar Colombia suna nan da rai.

Jami'an da suka ki yarda a bayyana sunayensu, sun fada jiya alhamis cewa kwanakin baya hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayya ta samu wannan faifan bidiyo, wanda a ciki aka ga Amurka, kuma a bisa dukkan alamu suna cikin koshin lafiya.

Ba a san ko yaushe ne aka dauki wannan hoton bidiyo ba.

Wadannan 'yan tawaye da aka fi sani da sunan FARC sun sace 'yan kwangilar na ma'aikatar tsaron Amurka a kudancin Colombia, a bayan da jirginsu na leken asiri dake laluben gonakin da ake shuka sinadarin hodar iblis ta Cocaine yayi saukar babu zato babu tsammani.

'Yan tawayen sun kashe Ba-Amurke na hudu da wani saje na sojojin Colombia dake cikin jirgin.

XS
SM
MD
LG