Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rwanda Tayi Watsi Da Zargin Magudin Da Tarayyar Turai Ta Gabatar - 2003-08-29


Jami'an zabe na kasar Rwanda sun yi watsi da sukar da Tarayyar Turai ta yi, cewar an yi ha'inci a lokacin zaben shugaban kasar da aka gudanar cikin makon nan a kasar dake yankin tsakiyar Afirka.

Shugaban hukumar zabe ta kasa, Chrysologue Karangwa, ya ce 'yan kallon Tarayyar Turai sun kasa gabatar da shaidar magudin da suka ce an yi, yana mai zargin kungiyar da nuna son kai.

Hukumar zaben ta ayyana shugaba Paul Kagame, dan kabilar 'yan tsiraru ta Tutsi, a zaman wanda ya lashe zaben na ranar litinin da gagarumin rinjaye. Hukumar ta ce Mr. Kagame ya alshe kashi casa'in da biyar daga cikin dari na dukkan kuri'un da aka jefa.

Babban dan takarar hamayya, kuma dan kabilar Hutu masu rinjaye a kasar, Faustin Twagiramungu, yana can baya da kashi uku kacal da dan dori daga cikin dari na kuri'un a cewar wannan hukuma.

A ranar laraba, tawagar 'yan kallon zabe ta Tarayyar Turai ta ce an tabka magudi a lokacin wannan zaben shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG