Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rahotanni Sun Ce Koriya Ta Arewa Tayi Barazanar Gudanar Da Gwajin Nukiliya - 2003-08-29


An shiga rana ta uku, kuma ta karshe, ta tattaunawar da ake yi kan shirin nukiliya na Koriya ta Arewa, yayin da ake samun rahotannin cewa kasar ta yi barazanar zata ayyana kanta a zaman mai makaman nukiliya.

Wakilai daga China, da kasashen Koriya biyu, watau Arewa da Kudu, da Amurka da Japan da kuma Rasha, za su bayar da sanarwar hadin guiwa a bayan ganawar da za su yi yau Jumma'a a birnin Beijing. Jami'ai suka ce bangarorin za su bayyana cewa sun yarda za su gana nan da watanni biyu, watakila a wannan karon ma a babban birnin na China.

Jim kadan a bayan da aka koma kan shawarwarin, kamfanin dillancin labaran Koriya ta Arewa ya bayar da wani rahoton dake cewa manufar kiyayyar da Amurka take nunawa kasarsu tana iya gurgunta sake yin tattaunawa.

Rahotannin jiya alhamis sun ce Koriya ta Arewa ta yi barazanar zata ayyana kanta a azaman kasar da ta mallaki makaman nukiliya, zata kuma yi gwajin nukiliyar. An ce wakilin Koriya ta Arewa a zauren shawarwarin, Kim Yong Il, shine yayi wannan furuci.

Wata mai magana da yawun fadar shugaban Amurka ta White House ta fada jiya alhamis cewa al'adar Koriya ta Arewa ce ta yi kalamun na neman harzuka wasu.

Kafofin labarai na Koriya ta Kudu sun ce Koriya ta Arewa ta gabatar da shawarar kulla yarjejeniya mai matakai hudu domin warware rikicin nukiliyar ciki har da yarjejeniyar cewa Amurka ba zata kai mata farmaki nan gaba ba, tare da kulla cikakkiyar huldar jakadanci a tsakanin kasashen biyu.

XS
SM
MD
LG