Sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka ta Yamma da jami'an jakadancin kasashen yammaci sun ziyarci birnin Buchanan mai tashar jiragen ruwa, wanda kuma ke hannun 'yan tawaye, a wani yunkuri na kawo karshen fadan da ake ci gaba da yi a tsakanin mayakan 'yan tawaye da na gwamnati.
Birnin na Buchanan yana hannun karamar kungiyar 'yan tawayen Liberiya da aka fi sani da sunan "MODEL" a takaice.
Daga cikin jami'an da suka ziyarci tashar jiragen ruwan birnin a jiya Jumma'a har da jakadan Amurka a Liberiya, John Blaney.
Mr. Blaney ya ce makasudin wannan ziyara da suka kai Buchanan shi ne tuntubar 'yan tawayen domin bude hanyar kai kayayyakin agaji na jinkai da ake matukar bukata a wannan yanki. Har ila yau ya ce za a tattauna yadda za a girka sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka ta Yamma nan gaba a yankin.
A halin da ake ciki dai, wani babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya ce ana bukatar karin 'yan kiyaye zaman lafiya har dubu 15 a kasar Liberiya domin tabbatar da tsaron ma'aikatan agaji.
A yanzu haka dai, sojojin Nijeriya su dubu daya da dari biyar ne kawai suke can Liberiya. Akasarin ma'aikatan agaji sun kasa rarraba kayayyakin masarufi a wajen Monrovia, babban birnin kasar, a saboda fargabar tsaro.