Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Lahadi Za A Ci Gaba Da Zaben Kananan Hukumomi Da Yankuna A Zimbabwe - 2003-08-31


A yau lahadi Zimbabwe zata ci gaba da gudanar da zabe a rana ta biyu, bayan da aka samu rahoton rashin fitowar jama'a da zarge-zargen tashin hankali da cin zarafin jama'a a ranar farko ta jefa kuri'u jiya asabar.

Jami'an rumfunan zabe suka ce mutane kalilan ne suka yi layi jiya asabar domin jefa kuri'unsu. An bayar da rahoton dogayen layuka a bankunan kasar ta Zimbabwe yayin da jama'a suka yi ta kokarin mika takardun ceki na albashinsu domin a basu tsabar kudi, yayin da kasar take fama da karancin takardun kudi.

Madugun 'yan adawa, Morgan Tsvangirai, ya ce jama'a sun fi damuwa da yadda za su biya bukatunsu na rayuwa a kan zuwa jefa kuri'a.

A halin da ake ciki, wani kakakin jam'iyyar MDC ta Mr. Tsvangirai ya ce an samu rahotannin tashin hankali da kuma kuntatawa masu jefa kuri'a a wurare da dama. Jami'an zabe na Zimbabwe suka ce ana gudanar da wannan aiki kusan ba tare da wani tashin hankali ba.

XS
SM
MD
LG