Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Laurent Gbagbo Ya Bukaci Firayim Minista Ya Mika Sunayen Wadanda Za A Nada Ministoci Na Wasu Ma'aikatu Biyu - 2003-08-31


Shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast ya bukaci firayim ministan kasar da ya gabatar da sunayen mutanen da za a nemi nadawa shugabannin wasu muhimman ma'aikatu biyu, nadin dake da matukar muhimmanci wajen tabbatar da dorewar sabuwar gwamnatin hadin kan kasa da aka kafa.

A cikin wata sanarwar da aka bayar jiya asabar, shugaba Gbagbo ya bukaci firayim minista Seydou Diarra da ya gabatar da sunayen wadanda za a iya nadawa a matsayin ministocin tsaron kasa da tsaron cikin gida ba tare da jinkiri ba.

An shirya cewar majalisar zartaswar gwamnatin hadin kan kasa ta Ivory Coast zata gana jibi talata.

'Yan tawayen Ivory Coast da jami'an gwamnati sun kasa cimma daidaiton ra'ayi a kan mutanen da za a nada shugabancin wadannan ma'aikatu tun lokacin da suka yi na'am da wata yarjejeniyar zaman lafiyar da Faransa ta shiga tsakani aka kulla a watan Janairu.

Yakin basasa ya barke cikin watan Satumbar bara a Ivory Coast a bayan da 'ya tawaye suka yi kokarin hambarar da shugaba Gbagbo.

XS
SM
MD
LG