Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Ciniki ta Duniya Ta Cimma Daidaituwa Kan Kofen Magunguna - 2003-08-31


Hukumar Ciniki ta Duniya, WTO, ta yarda zata kyale kasashe matalauta su ringa sayo kofen magungunan da kamfanonin da suka kirkiro su suka yi rajistar hana wani yin kofe ko sayar da su.

Wannan yarjejeniya da aka cimma a jiya asabar, zata taimaka wa kasashen dake fama da talauci wajen yakar munanan cututtuka kamar kanjamau da zazzabin maleriya.

Jami'ai sun kammala zayyana wannan yarjejeniya a rana ta shida a jere da aka yi ana ganawa a birnin Geneva.

Wannan matakin zai sassauto da dokokin hana yin wani kofen abinda wani ya kirkiro ta yadda kasashe matalauta da ba su da masana'antun sarrafa magunguna zasu iya sayo kofe mai rahusa na magunguna masu tsada domin yakar munanan cututtuka.

Ci gaban da aka samu wajen amincewa da yarjejeniyar jiya asabar, ya zo a bayan rokon da kasashen Afirka suka yi ga masu yin adawa da wannan matakin da su sake tunani.

Amma duk da haka, wasu kungiyoyin agaji sun ce wannan yarjejeniya ba zata sassauto da nauyin marasa lafiya wadanda suka fi fama da talauci ba.

XS
SM
MD
LG