Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Tara Sun Mutu Lokacin Da Jirgin yakin Karkashin Ruwa Na Rasha Ya Nutse - 2003-08-31


Sojojin Rasha tara sun mutu jiya asabar a lokacin da wani tsohon jirgin yaki na karkashin ruwa mai aiki da nukiliya ya nutse cikin tekun Barents, lokacin da ake jansa zuwa wani dandalin kera jiragen ruwa inda za a kwakkwance gabobinsa.

Jami'ai sun fada jiya asabar cewar mutum daya ne kawai daga cikin mutane 10 dake cikin wannan jirgi aka ceto.

An gano gawarwaki biyu.

Wannan jirgin karkashin ruwa da aka kera shekaru 40 da suka shige ya nutse jiya asabar da safe a dab da tsibirin Kildin dake kusa da tashar jiragen ruwan Murmansk, lokacin da wani hadari mai iska ya tsinka wasu robobin da ake amfani da su kamar tayu wajen jan jirgin a kan teku.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce za a binciki musabbabin wannan bala'in.

Jami'ai suka ce injin wannan jirgi mai aiki da nukiliya ba ya kunne, kuma ba ya yin wata barazana ga muhalli.

Amma 'yan rajin kare muhalli sun yi kashedin cewa tana yiwuwa iska mai guba ta tsiyaye daga cikin injin.

XS
SM
MD
LG