Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Afghanistan Da Na Amurka Suna Yakar 'Yan Taleban - 2003-08-31


Ana gwabza kazamin fada a kudu maso gabashin Afghanistan domin kawar da mayakan Taleban su kimanin dubu daya daga cikin wuraren buyarsu a cikin duwatsu.

A cikin mako gudan da ya shige, sojojin Afghanistan dake samun tallafin sojojin Amurka sun akshe mayakan Taleban 33 a fadan da sojojin na Amurka suka bayyanada cewa yana yin zafi a wasu lokutan.

An fara gwabzawa a bayan da jiragen saman kai farmakin bam na Amurka suka yi ta ruwan bama-bamai a duwatsun Chinaran dake lardin Zabul.

A yanzu kuma, jiragen kai farmaki da helkwaftoci na Amurka suna dafawa sojojin kasa na Afghanistan da zaratan sojojin Amurka dake kokarin shiga cikin wadannan duwatsu.

Wannan fadan ya biyo bayan karuwar hare-haren da 'yan Taleban ke kaiwa da nufin gurgunta gwamnatin shugaba Hamid Karzai.

XS
SM
MD
LG