Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obasanjo Na Nijeriya Zai Ziyarci Kasar Liberiya - 2003-09-01


Ana sa ran shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya zai sauka yau litinin a kasar Liberiya domin gajeruwar ziyara da nufin karfafa shirin wanzar da zaman lafiya a kasar.

Ana sa ran shugaba Obasanjo zai gana da shugabannin gwamnatin rikon kwarya ta Liberiya da na Majalisar Dinkin Duniya, MDD.

Wannan ziyara ta sa ta zo makonni uku a bayan da shugaba Charles taylor na Liberiya yayi murabus yayi gudun hijira zuwa Nijeriya, a wani bangare na yarjejeniyar da aka cimma da nufin kawo karshen yakin basasar shekaru hudu. Mr. Taylor yayi murabus a saboda matsin lambar kasashen yammacin Afirka da na yammacin Turai da kuma 'yan tawayen da suka hana shi sakat.

A ranar Jumma'a, sojojin kiyaye zaman lafiyar da Nijeriya ke jagoranci, sun shiga Buchanan, birni na biyu wajen girma a Liberiya, wanda ke hannun 'yan tawaye, a matakin farko na girka 'yan kiyaye zaman lafiya na dindindin a can.

A cikin wata gudan da ya shige, an girka sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka ta Yamma, akasarinsu sojojin Nijeriya su dubu 1 da 500 a Liberiya, inda aka dora musu alhakin tabbatar da yin aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a tsakanin gwamnatin rikon kwarya da kungiyoyin 'yan tawaye biyu.

XS
SM
MD
LG