Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar MDD Zata Karbi Aikin Kiyaye Zaman Lafiya A Kwango-Ta-Kinshasa - 2003-09-01


An shirya cewa a yau litinin wata runduna ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD, za ta karbi ayyukan kiyaye zaman lafiya a lardin Ituri mai fama da yaki a kasar Kwango-ta-Kinshasa.

A jiya lahadi, wata rundunar tarayyar Turai da Faransa take yi wa jagoranci, ta mika sansaninta na karshe dake kusa da Bunia, babban birnin lardin, ga sojojin MDD 'yan kasar Bangladesh.

Rundunar sojojin MDD ta Ituri za ta kunshi sojoji dubu 4 da 800, akasarinsu daga kasashen Nepal, Bangladesh da Pakistan.

Wannan runduna da ake kira "Birged din Ituri" an dora mata alhakin hana fadace-fadacen kabilancin da a cewar wasu kafofi, yayi sanadin mutuwar mutane har dubu 50 cikin shekaru hudun da suka shige.

Faransawa sun mika sansanin na karshe jiya lahadi a daidai lokacin da ake samun rahotannin barkewar sabon fada na kabilanci a wani wuri mai tazarar kilomita 70 a arewa maso yamma da Bunia.

XS
SM
MD
LG