Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Suna Binciken Sabon Fadan Da Aka Ce Ya Barke A Liberiya - 2003-09-05


Wasu sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka ta Yamma dake Liberiya sun yi tattaki zuwa arewacin kasar domin binciko rahotannin barkewar wani fadan da ka iya wargaza yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla kwanakin baya.

Wani kakakin sojojin, Kanar Theopilus Tawiah, ya ce jiya alhamis suka bar Monrovia domin zuwa Totota, mai tazarar kilomita 100 daga babban birnin.

A ranar laraba dubban 'yan gudun hijira suka bar sansanoninsu a yankin Totota bayan da suka ji kararrakin fashe-fashen manyan bindigogi da kuma rade-radin barkewar sabon fada. Akwai 'yan Liberiya kimanin dubu 60 cikin wadannan sansanoni, dukkansu wadanda suka gujewa gidajensu a sanadin yakin basasar da aka yi shekaru 14 ana gwabzawa a kasar.

An ci gaba da samun rahotannin fadace-fadace a yankunan karkara na Liberiya, duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da kungiyoyin 'yan tawaye biyu tare da gwamnati suka sanyawa hannu a ranar 18 ga watan Agusta.

Har ila yau a jiya alhamis, hukumar kiwon lafiya ta duniya ta yi kashedin cewa Liberiya tana fuskantar mummunar matsalar barkewar annoba, inda ake samun karuwar rahotannin bullar cututtukan kwalara da atuni.

XS
SM
MD
LG