Shugaban babbar kungiyar 'yan tawayen kasar Sudan da wani babban jami'in gwamnati za su gana yau Jumma'a a kasar Kenya, domin tattaunawa da nufin kawo karshen yakin basasar shekaru 20 a kasarsu.
Wannan tattaunawa da za a yi a tsakanin madugun kungiyar 'yan tawayen SPLA, John Garang, da mataimakin shugaban Sudan, Ali Osman Mohammed Taha, za a gudanar a garin Naivasha na Kenya.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, yayi marhabin da wannan ganawa, ya kuma bayyana fatan cewa bangarorin biyu zasu cimma shirin zaman lafiya cikakke.
Ana yakin basasa a Sudan a tsakanin mutanen kudancin kasar wadanda akasarinsu Kiristoi ne da masu bin addinan gargajiya, da kuma na arewacin kasar wadanda akasari Musulmi ne kuma larabawa.
Mutane miliyan biyu aka yi kiyasin cewa sun mutu awannan rikici, amma akasarinsu a saboda cututtuka ne da kuma bala'in yunwar da suka faru a sanadin yakin.