Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jami'in Amurka Ya Ce Za A Ga Sakamako Maras Kyau Idan Koriya Ta Arewa Ta yi Gwajin Makamin Nukiliya - 2003-09-05


Wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya ce za a ga "sakamako maras kyau" idan har Koriya ta Arewa ta yi aiki da barazanar da aka ce ta yi ta gwajin makamin nukiliya.

Jami'in da ya ki yarda a bayyana sunansa ya ce tattaunawar da za a iya yi nan gaba kan lallashin Koriya ta Arewa ta watsar da shirinta na nukiliya tana iya fuskantar matsala idan har ta yi gwajin makamin nukiliya.

Ya ce yin gwajin zai kuma yi illa ta wasu hanyoyin da bai fayyace ba.

Koriya ta Arewa ba ta fito da bakinta ta yarda cewar ta yi wannan barazana ba, barazanar da jami'an Amurka suka ce wakilan Koriya ta Arewa ne suka yi a wajen tattaunawar da aka yi makon jiya a Beijing.

Jami'in na Amurka ya bayyana tattaunawar a zaman harsashi mai kyau wajen warware batun nukiliya na Koriya ta Arewa, amma ya ce har yanzu da sauran aiki a gaba.

XS
SM
MD
LG