Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Da Jamus Sun Ce Majalisar Dinkin Duniya Tana Bukatar Karin Iko A Iraqi - 2003-09-05


Shugabannin Faransa da Jamus sun yi watsi da sabon kudurin da Amurka ta zana kan Iraqi a gaban Majalisar Dinkin Duniya, MDD, suna masu fadin cewa a karkashinsa ba za a mayar da ikon siyasa hannun gwamnati ta 'yan Iraqi da sauri ba.

Wazirin Jamus, Gerhard Schroeder, da shugaba Jacques Chirac na Faransa sun fada a jiya alhamis cewar kudurin bai kuma bai wa MDD ikon taka rawar da ya kamata ba a Iraqi.

Suka ce suna fata Amurka za ta yarda da yin sauyi a daftarin kudurin.

Wannan daftarin kudurin da Amurka ta zana yayi kiran da a kafa rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasa da kasa a karkashin ikon jagorancin Amurka.

Har ila yau kudurin yayi kira ga majalisar mulkin da Amurka ta nada a Iraqi da ta yi aiki tare da jami'an Amurka da na MDD wajen tsara lokutan gudanar da zabe da zana sabon tsarin mulki wa Iraqi. Amma kuma kudurin ya bar ikon harkokin siyasa da na soja na Iraqi daram a hannun Amurka.

A yau jumma'a wakilan Kwamitin Sulhun majalisar zasu gana da juna kan wannan daftarin kuduri.

Wannan lamari yana zuwa a daidai lokacin da sakataren tsaron Amurka, Donald Rumsfeld ya ziyarci Iraqi jiya alhamis, domin ganawa da kwamandoji da sojojin Amurka. Ya shaidawa 'yan jarida cewar yana son ganin karin sojoji na Iraqi da na wasu kasashen duniya, amma kuma ba na Amurka ba, a cikin kasar ta Iraqi domin karfafa tsaro.

XS
SM
MD
LG